Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da cewa jami’anta uku sun samu muƙaman fasaha da kuma shaidar ƙwarewa daga Hukumar Kwastam ta Duniya (WCO), lamarin da ke ƙara ƙarfafa wakilcin Najeriya a harkokin kwastam na ƙasa da ƙasa.

Ɗaya daga cikin jami’an, Mataimakin Kwanturola Ahmed Labaran, an zaɓe shi domin yin aiki na tsawon shekaru uku a matsayin mai ba da shawara kan harkokin fasaha a sashen yaƙi da laifuffuka na hukumar, da ke Brussels, Belgium.

Haka kuma, Mataimakiyar Kwanturola Nnenna Ugo Awa ta samu shaidar ƙwarewa a matsayin mai ba da shawara kan fasaha da ayyuka na shirye-shiryen Authorised Economic Operator (AEO), bayan halartar horo a Afirka ta Kudu da kuma aikin tantance shirye-shiryen a Laberiya.

A gefe guda, Hukumar Kwastam ta Duniya ta amince da tura Mataimakiyar Kwanturola Lauretta Utubor zuwa sashen kula da manufofin rarraba kayayyaki na hukumar da ke Brussels, inda za ta taimaka wajen bincike da samar da manufofi da ƙa’idojin kwastam na ƙasa da ƙasa.

Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi, ya taya jami’an murna, tare da jaddada aniyar hukumar na ƙara ƙarfafa ƙwarewar ma’aikatanta da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, domin inganta ayyukanta da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *