Kamfanin Dangote Coal Mines Limited da ke Jihar Kogi ya bayar da tallafin karatu na miliyoyin naira ga ɗalibai 42 daga al’ummomin da ke maƙwabtaka da wurin haƙar ma’adininsa, na shekarar karatu ta 2026/2027.

Kamfanin ya ce tallafin na daga cikin shirye-shiryen kyautata zamantakewarsa (CSR), da kuma cika yarjejeniyar bunƙasa al’umma da ya ƙulla da mazauna yankin, domin sauƙaƙa musu samun ilimi da ƙarfafa ci gaban matasa.

Al’ummomin da suka amfana da tallafin sun haɗa da Awo-Akpali, Awo-Ojuwo, Awo-Akpolokuta, Awo-Atte, Onupi da Ajobe-Ofeanyaka, waɗanda duk ke Ƙaramar Hukumar Ankpa ta Jihar Kogi.

Shugaban al’ummar Awo-Akpali, Dakta Samuel Adejoh, wanda ya yi magana a madadin sauran al’ummomin da suka amfana, ya yaba wa kamfanin bisa cika alƙawarin da ya ɗauka, yana mai cewa tallafin zai rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin kuɗin karatu.

A wani mataki makamancin haka, kamfanin ya kuma biya kuɗin haya na shekara-shekara ga masu filaye a al’ummomin Awo-Akpali, Awo-Ojuwo da Awo-Akpolokuta, inda waɗanda suka amfana suka yaba da biyan kuɗin cikin lokaci, tare da roƙon kamfanin ya ci gaba da hakan.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *