Hakan na zuwa ne bayan Tinubu ya bayyana a wani taro a Mapo Hall da ke Ibadan cewa ya kamata ’yan Najeriya su manta da batun tallafin man fetur, domin wannan tsari ya zama tarihi.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar yaƙin neman zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ya ce cire tallafin ba tare da ingantaccen shiri da matakan rage wa talakawa raɗaɗi ba, ya jefa jama’a cikin tsadar sufuri, hauhawar farashin abinci da ƙarin talauci.
- PDP ta ƙaryata shiga haɗakar ƙungiyoyin adawa, ta ce ba za ta halarci taron 30 ga Nuwamba ba
- Gwamnatin Jihar Kano za ta yi wa yara miliyan biyu rigakafi
Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen sauraron koken jama’a da gyara manufofin tattalin arziƙinta, tare da nuna damuwa kan abin da ya kira raunana muhimman hukumomin dimokuraɗiyya domin cimma muradin wa’adin mulki na biyu.
ADC ta bayyana ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda take ganin zai iya farfaɗo da tattalin arziƙi da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya, sannan ta buƙaci ’yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen kawo sauyin shugabanci.