Sanata Binos Dauda Yaroe, mai wakiltar Kudancin Adamawa a Majalisar Dattawa, ya bayyana dalilansa na fita daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar ADC.
Ya ce biyayyarsa ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da kuma kishin dorewar hamayya a siyasar Najeriya ne suka sa shi daukar wannan mataki.
Sanatan ya ki amincewa da zabin bin sahun Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Maimakon haka, Yaroe ya zabi ya koma ADC, inda Atiku Abubakar yake taka rawar gani a matsayin daya daga cikin jagororin gamayyar jam’iyyun adawa da ke tasowa.
Yayin da yake tattaunawa da manema labarai, Sanata Yaroe ya jaddada cewa godiya da kuma riko da akidun dimokuradiyya ne suka sanya shi yanke shawarar hakan.
Ya ce: “Ina tare da Atiku Abubakar tun farkon tafiyata ta siyasa.
“Ni ba mutumin da yake mantawa da mutanen da suka tsaya mini a lokacin wahala ba ne.”
Ya kuma ce Atiku ne ya ba shi gagarumin tallafi lokacin zaben fidda gwani na Sanata a PDP a shekarar 2019, da kuma sake zabensa da aka yi a shekarar 2023.
“Ba zai yiwu dukkanmu mu koma jam’iyya mai mulki ba.
“Idan kuwa kowa ya koma APC, to babu sauran adawa a kasar nan.
“Dimokuradiyya tana bunkasa ne kawai idan akwai kakkarfar murya da za ta iya kalubalantar mahukunta,” in ji Yaroe.
Sanata Yaroe daya ne daga cikin sanatoci tara da suka fice zuwa jam’iyyar ADC a ranar 12 ga Maris, 2026, wanda hakan ya kasance babban sauyi a taswirar siyasar kasar da aka sanar a zauren majalisar dattawa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.