arangama tsakanin yansandan pakistan da masu zanga zanga tayi ajalin mutane 11

Akalla mutane 11 sun mutu yayin da wasu 70 suka yi raunuka bayan barkewar rikici a tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar Pakistan.

‘Yan sanda a yankin sun ce masu zanga-zangar a ƙarkashin ƙungiyar farar hula ta Awami Action Committee, wadda take gwagwarmayar ƙwato wa yankin ‘yanci ta fuskar siyasa da tattalin arziki, sun taru ne a gaban ɗakin ajiye gawa da ke babban asbitin yankin, inda aka ajiye gawar daya daga cikin su wanda jami’an tsaro suka kashe.

Kwamishinan ‘Yan Sandan yankin, Sardar Waheed Khan, ya ce su ma masu zanga-zangar sun yi ajalin ‘yan sanda huɗu, lamarin da ya ce ya sa jami’an tsaro yin amfani da ƙarfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Babban Sufeton ‘Yan sanda na yankin Liaqat Malik ya ce ƴan sanda 23 na cikin mutane 50 ɗin da suka jikkata a sakamakon arangamar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *