Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabon Ministan Lantarki Mista Joseph Tegbe, da kuma Karamin Ministan Harkokin Waje Sola Enikanolaiye.
An gudanar da kwarya-kwaryar bikin rantsarwar ne ranar Litinin a Fadar Shugaban Kasa, wanda ya samu halartar Ministoci da Manyan Jami’an gwamnati, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban a bangaren labarai Bayo Onanuga, ya bayyana.
-
NLC Da TUC sun yi barazanar tsunduma yajin aiki
-
Gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da murkushe ‘Yan Ta’adda
Onanuga yace biyo bayan murabus din da tsaffin Ministocin Harkokin Waje da na Lantarki suka yi a watannin baya, Shugaban Kasa ya gabatar wa Majalisar Dattawa bukatar cike gibin da suka bari.
A ranar Laraba, 6 ga Mayu ne Majalisar ta tantance sabbin Ministocin, tare da sahalewa shugaban ya nada su mukaman guda biyu, domin cike gibin da ke akwai.