Hukumar Kwallon Kafa ta duniya FIFA, ta magantu game da hana Alkalin wasa Omar Abdulkadir Artan, shiga Amurka.

Cikin wata sanarwa data wallafa, FIFA tace tattaunawar da suka yi da hukumomin Amurka,  na nuni da cewa Alkalin wasan dan asalin kasar Somaliya ba zai shiga kasar ba.

Ko da yake FIFA ba ta bayyana dalilan  da suka sanya Amurka daukar wannan mataki ba, Artan mai shekaru 34, na da cikakkiyar Bizar shiga a matsayin sa na fitaccen mai alkalancin wasanni daga  Afirka.

“Dangane da wasannin FIFA, kasar da ke karbar bakunci ce ke da hurumin yanke hukuncin amincewa da bayar da Bisa ko  kuma bayar da damar shigowa cikinta,” in ji FIFA.

Matsayin na FIFA ya kawo karshen duk wani fata da ya rage cewa za ta iya sauyawa Amurka tunani game da batun kafin fara gasar.

Lamarin dai ya haddasa muhawara mai zafi a fadin duniyar kwallon kafa, inda mutane da yawa ke tambayar yadda za a iya hana jami’in da FIFA ta zaba shiga irin wannan babban wasa.

Kasar Somaliya na cikin kasashen da suka fi fuskantar takunkumin tafiye-tafiye da yawan aibatawa karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *