Babban Sufetan ‘Yan sanda na kasa, Tunji Disu ya umarci kwamishinonin Yan sandan jahohi da su fara daukan tsaurarar matakai kan motocin hawa marasa lamba.
IGP Disu ya ba da wannan umarni ne yayin taron Wata-Wata da ya jagoranta da Kwamishinonin Rundunar na jihohi, da ya gudana ranar Talata a Cibiyar Zaman Lafiya ta Goodluck Ebele Jonathan da ke Shalkwatar ta a Abuja.
Sufetan ‘Yan Sandan ya umarci manyan jami’an rundunar da su tashi tsaye wajen kama duk wata mota da babu lamba a jikinta ko kuma aka ɓoye lambar, a matsayin wani ɓangare na matakan ko-ta-kwana na magance matsalolin tsaro da ke fuskantar ƙasar.
-
Yaɗa Bayanan Ƙarya na Barazana ga Tsaro – Janar Waidi Sha’aibu
-
Dalilin da ya sa Najeriya ta kasa shawo kan Ta’addanci — Moghalu
Disu, yace ƙasar na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashin teku da na kan tudu, rikicin kungiyar Asiri, ta’addanci, fashi da makami, rikicin manoma da makiyaya, da kuma laifuka ta intanet.
Ya bayyana cewa daukar matakin haramtawa da kuma kama motocin da ba bu lamba, na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen dakile zirga-zirgar miyagu a tsakanin Al’umma.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar shugabanci na gari, ingantaccen haɗin kai, da kuma amfani da bayanan sirri domin rundunar ta kasance kan gaba, wajen hana masu aikata laifi sakat.