Kwamishinan, yace lokaci da Rundunar zata hana masu aikata laifi motsawa a Jihar

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaki da laifuka bayan ta cafke mutane 345 da ake zargi da daba, safarar miyagun kwayoyi da sauran ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan wani samame na musamman da aka gudanar a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, inda jami’ai suka kai farmaki maboyar masu laifi da wuraren safarar miyagun kwayoyi.

A cewarsa, mutane 187 daga cikin wadanda aka kama sun fada hannu ne yayin aikin share fage na kwanaki uku, yayin da sauran aka cafke su a wasu samame da bincike da rundunar ke ci gaba da gudanarwa.

Bakori ya ce ana ci gaba da yi wa wadanda ake zargin tambayoyi, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a aikata laifuka.

Baya ga kamen, rundunar ta kwato makamai masu hadari guda 270 da suka hada da wukake, adduna da kulake, tare da tarin miyagun kwayoyi irin su cannabis, kwayoyin Exol da kuma hadadden abin maye da aka fi sani da “Suck and Die.”

Kwamishinan ya danganta wannan nasara ga Operation Kukan Kura da sabon sashen Violent Crime Response Unit (VCRU), wadanda suka taimaka wajen kara karfin sintiri da mayar da martani cikin gaggawa.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ga masu aikata laifuka ba, domin za a ci gaba da matsa musu lamba har sai an dakile ayyukansu gaba daya.

Bakori ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa goyon bayan da take bai wa jami’an tsaro, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan sirri, yana mai tabbatar da cewa za a rika kare sirrin duk wanda ya bayar da bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *