Asusun bada lamuni na duniya IMF ya tabbatarwa da cewa tattalin arzikin Najeriya na ci gaba cikin wani rahoto daya fitar
IMF ta yaba da gyare-gyaren tattalin arziki da aka aiwatar a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton ya nuna cewa matakan da gwamnatin shugaba Tunubu ta dauka da suka hada da dakatar da tallafin mai, bude kasuwar musayar kudaden waje, da tsaurara ka’idojin kudi sun taimaka wajen dawo da kwarin gwiwa ga masu zuba jari da karfafa tsaron tattalin arziki.
- Gwamnatin tarayya zata fara biyan kananan ’yan kwangila bashi
- Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana
- Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
IMF yace Gwamnatin Tarayya ta nuna jajircewarta wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar tallafawa masu rauni, kananan masana’antu, noma, ilimi da samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.
Haka zalika, IMF ta yi hasashen bunkasar tattalin arzikin Najeriya a matsakaicin lokaci, tare da bunkasar ajiyar kudaden waje, karuwar jarin kudaden shiga, da karfafa kudaden haraji.
Gwamnatin Najeriya dai tayi maraba da rahoton na IMF tare da alwashin ci gaba da daukar matakan da suka kamata don tabbatar da dorewar tattalin arzikin kasar.
