Hukumar Kula da Almajirai da Yaran da ba su zuwa Makaranta (NCAOOSCE) ta ce  kimanin Almajirai da masu karamin karfi dubu  90 ne suka rabauta da naman Salla a bana.

Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ta Nura Muhammad ya aikewa manema labarai, yace Makarantun Tsangaya 750 ne suka amfana a Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Nasarawa, Neja, Kaduna, Bauchi, Filato da Yobe.

Sanarwar tace ta samu hadin kai daga Malaman Tsangayu, lamarin da ya kai ga samun nasarar aikin cikin tsari.

Ta jaddada aniyar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta walwala, haɗin kai da ci gaban Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan.

An gudanar da wannan shiri ne tare da tallafin kungiyar bada tallafi ta (Fountain Humanitarian Foundation) da (Türkiye Diyanet Foundation) a cewar hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *