Farashin gawayin girki na ci gaba da hauhawa sakamakon tashin gwauron zabin da farashin Iskar gas din griki keyi a Najeriya.

Magidanta da dama a Najeriyar na komawa amfani da gawayi wajen girki, sakamakon tashin gwauron zabin da farashin makamashin iskar gas ta girki ya yi a baya-bayan nan.

A jihohin Kaduna da Kano da Ondo da Kwara, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, magidanta na ci gaba da kokawa kan yadda farashin iskar gas da kuma na gawayin girki ke ci gaba da tashi.

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar Laraba ya nuna cewa binciken da ta gudanar a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, ya bayyana cewa farashin makamashin iskar gas ya yi tashi.

Haka kuma binciken ya gano cewa hatta ana fuskantar karancin Gas din a wasu gurare, lamarin da ya haddasa karuwar bukatar gawayin girki da kuma tashin farashinsa.

A halin yanzu, ana sayar da kilo guda na iskar gas kan naira 1,700, yayin da cika silinda mai nauyin kilo 12.5 ke kai wa naira 21,250.

Wani mai sayar da iskar gas, Abdul Alhaji, ya danganta tashin farashin da rikicin da ke ci gaba da ruruwa a Gabas ta Tsakiya.

“Kafin rikicin Iran da Isra’ila ya tsananta, muna sayar da kilo guda kan naira 920. Amma tun daga lokacin farashin ke ci gaba da hawa kusan a kullum har ya kai naira 1,700 a yanzu.”

A makon da ya gabata ne Najeriya da kasashen Nijar da Aljeriya suka yi wani bikin shimfida layin dogo, da zai kai Iskar Gas zuwa Aljeriya ta cikin Nijar, domin siyarwa ga Nahiyar Turai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *