Dan wasan gaba na kasar Faransa, Kylian Mbappé, na da damar karya manya-manyan tarihi da aka kafa a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na 2026.
Za a fara gasar ne ranar Laraba, 11 ga watan Yuni, inda daya daga cikin masu masaukin baki, Mexico za ta yi sharar fage da kasar Afirka ta kudu.
Faransa za ta bude wasanta ne da kasar Senegal a ranar 16 ga watan Yuni.
Idan Mbappé ya iya zura kwallaye biyu a gasar ta bana, zai zama wanda ya fi kowa zura kwallo a tarihin tawagar maza ta Faransa, inda zai karya tarihin Olivier Giroud mai kwallaye 57.
Haka kuma zai zama wanda ya fi kowa zura kwallo a gasar cin kofin duniya ga Faransa, inda zai karya tarihin kwallaye 13 na Just Fontaine.
Idan Mbappé ya zura kwallaye biyar, zai zama wanda ya fi kowa zura kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya ta maza ta FIFA, inda zai karya tarihin kwallaye 16 na Miroslav Klose.
Kuma idan ya zura kwallo a wasan karshe, zai zama namiji na farko da ya taba zura kwallaye biyar a wasannin karshe na gasar cin kofin duniya.
Wannan ne tarihin da masu sharhi ke ganin cewa Mbappé zai iya karya su da kuma ajiye sabon tarihi.
Ko me nene ra’ayin ku kan hakan?