Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa hare-haren Isra’ila kan kasashen Siriya da Lebanon sun kai matakin da suke barazana ga kasarsa

Erdogan yace yana ganin hakan a matsayin barazana ga zaman lafiyar duniya, domin haka ya dace a kawo karshen lamarin

Shugaban ya shaida wa majalisar  dokokin Kasarsa  cewa gwamnatin Isra’ila karkashin Firaminista Benjamin Netanyahu ta zama ‘yar ina da yaki.

Ita dai Turkiyya ta kasance a gaba-gaba wajen caccakar manufofin Isra’ila na yakin da ke faruwa a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, da abin da ke faruwa a Lebanon gami da yaki da Iran.

Shugana Erdogan ya bukaci kasashen duniya su tashi tsaye wajen tabbatar da samun zaman lafiya a duniya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *