Portugal ta lallasa Najeriya da ci 2-1 a wasan sada zumunta na kasa da kasa yayin da kasar ta kammala shirye-shiryen ta na gasar cin kofin duniya da nasara ta biyu a jere.
Pedro Neto ne ya ci wa Portugal kwallo ta farko kafin Akor Adams ya ramawa Super Eagles.
-
Mbappé na da damar karya manyan tarihi 4 a gasar Kofin Duniya ta 2026
-
Rashford zai koma Manchester United
Sai dai, Portugal ta sake dawowa kan gaba ta hannun Francisco Conceição, wanda ya lankwasa kwallo mai kyau zuwa kusurwa, don tabbatar da nasara ga masu masaukin baki.
Nasarar ta karawa Portugal kwarin gwiwar shiga gasar cin kofin duniya bayan samun nasara a jere.
