Daruruwan Hausawa ne a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, suka fito kan tituna ranar Laraba, a wata zanga-zangar nuna bacin rai da abinda suka ce ana musu.
Masu zanga-zangar sun bayyana takaicinsu kan yadda ake dora laifin ayyukan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kan daukacin Hausawa.
Shugabannin al’ummar Hausawa mazauna Birnin na Badin, sun ce aikin wasu tsirarun masu aikata laifi bai kamata ya shafi sauran kabila baki daya ba.
“Hausawa masu bin doka ne, kuma masu son zaman lafiya ne” Inji masu zanga-zangar.”
- Sirika – Shaidu sun bayyana Yadda aka yaudari Al’umma da jirgin Ethiopia
- Gwamnatin Edo ta rufe makarantu saboda barazanar tsaro
- Da Dumi-Dumi: An harbe ’yan bindiga a Abuja
Zanga-zangar ta biyo bayan shafe makonni karkashin matsin lamba daga jami’an tsaro, da masu zanga-zangar ke cewa ya rikide zuwa cin zarafi, nuna wariya, da zarge-zarge marasa tushe.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 15 ga Mayu, 2026, wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji suka kai hare-hare lokaci guda, a makarantun Yawota da Ahoro-Esinele, a karamar hukumar Oriire ta Jihar Oyo inda suka sace mutane 46 da dalibai 39.