Masu zanga-zangar sun bukaci Al'umma su daina kawar da kai wajen yaki da tabarbarewar tsaro a Najeriya [Hoto:AI]

Masu Zangar Zangar dauke da kwalaye dake nuna kalamai na kwatar kai, tafe suna rera wakokin karfafa gwiwa, sunyi cirindo a filin unity fountain dake kan titin Shehu Shagari a Birnin Abuja.

Daruruwan Matasa da Dattawa ne daga kungiyoyin fararen hula, da suka yiwa gangamin lakabi da “Yan Najeriya sun hada kai domin yaki da ta’addanci, Rashin Tsaro bashi da Gurbi, daga kudu zuwa Arewa, Gabas zuwa Yamma.”

Masu Zanga Zangar sun ce sun shirya wannan gangami domin nuna bacin ransu game da yaduwar rashin tsaro, da kuma shaidawa gwamnatin Najeriya cewa al’umma ta gaji da matsalar.

Masu shirya gangamin sun bayar da ba’asin cewar akwai kasashe da suka shallake Najeriya fuskantar barazanar tsaro, amma yanzu ya zame musu tarihi, a saboda haka babu wanda zai fadawa yan Najeriya cewar rashin tsaro bashi da magani.

Kwamared Okwarachi Jacob, ya gabatar da jawaban a matsayin sa na Sakataren kungiyar, yace babu dalilin da zai sanya ana kashe makudan kudade a bangaren tsaro, kuma lamarin yana kara yaduwa.

A saboda haka suke kira ga gwamnatin tarayya da yan majalisu su duba lamarin nan tun da sauran lokaci, tunda matsalar al’umma bawai ta talauci bace a yanzu, ta tsaro ce da ke hana manoma komawa Gonakin su.

Shi kuwa shugaban gamayyar kungiyoyin da suka shirya zanga zangar Kwamared Igwe Udomata yayi tsokaci ne hadin kan Arewaci da Kudanci, Yammaci da Gabashin Najeriya.

A cewar sa anyi amfani da Kabilanci da Addini wajen raba kan al’umma domin cimma wasu manufofi, ana amfani da rashin tsaro wajen hallaka dubban al’umma kasa.

Yana mai dora alhakin hakan akan ‘Yan Siyasa dake siyasantar batun, tare da jefa  rayuwar al’umma cikin hadari.

“Lamarin akwai takaici matuka, maimakon yan siyasa su hada kai domin ceto mu daga barazanar tsaro, sun koma jifan junan su da laifi, bayan mu take shafa” Inji Kwamared Igwe Udomata.

Shi kuwa Dattijo Kennedy Tebuko cewa yayi lokaci yayi da yan Najeriya za su daina yaudarar kansu, ta hanyar hada karfi da karfe su yaki matsalar, bawai zubawa gwamnati ko jamian tsaro ido ba.

Dattijon yace masu shirya hare-hare sun lura da shayin da yan Najeriya ke nunawa game da su, shi yasa suke cin karen su babu babbaka, akan matsalar da idan aka mance da rabuwar kai za’a iya kawo karshen sa a kankanin lokaci.

Najeriya a baya bayan nan na fuskantar manyan matsaloli na tabarbarewar tsaro, garkuwa da mutane da Ta’addanci, duk da biliiyoyin kudade da kasar ke kashewa a kasafin kudin kowacce shekara, ba tare da biyan bukata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *