Rukunin farko na ’yan Najeriya daga Afirka ta Kudu sun sauka a Birni Ikko a ranar Alhamis.

Rukunin, wanda ya kunshi ’yan Najeriya 268, sun sauka da karfe 10:30 na safe a filin jirgin sama na Murtala Muhammed a jirgin Air Peace.

Da farko an shirya dawowar tasu ne a ranar Litinin, kafin daga bisani aka dage dawowar tasu zuwa ranar Laraba saboda jinkirin takardu.

Rahotanni sun ce sama da ’yan Najeriya Dubu 1 ne suka nuna sha’awar komawa gida daga Kasar Afirka ta Kudu.

Tuni Kasashen irinsu Ghana, Kenya, Uganda da Malawi suka yi wajen kwashe al’ummar su dake zaune a kasar, gabanin cikar wa’adin 31 ga watan Yuni da kasar ta baiwa baki su koma kasashen su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *