Zakarun duniya Ajantina sun ci gaba da rike matsayinsu na daya a sabon jadawalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), da aka fitar ranar Alhamis, inda suka kara karfafa matsayinsu gabanin gasar cin kofin duniya ta 2026.
Albiceleste na ci gaba da zama a kan kololuwa a duniyar kwallon kafa bayan samun nasarori masu kayatarwa a wasannin kasa da kasa na baya-bayan nan, yayin da Spain da Faransa ke matsayi na biyu da na uku bi da bi.
Ingila da Portugal ne suka kammala manyan biyar, sai Brazil a matsayi na shida.
Najeriya ta ci gaba da zama a matsayi na 26 a duniya. Super Eagles sun yi nasara a gasar Unity Cup da aka yi a Landan, inda suka doke Zimbabwe da Jamaica.
Maroko ce kasa mafi girma a Afirka a jadawalin, inda take matsayi na bakwai a duniya kuma ta ci gaba da riƙe matsayin ta.
Sabon jadawalin ya zo ne yayin da aka mayar da hankali kan gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, wadda Amurka, Mexico da Canada za su hada kai wajen karbar bakunci. Gasar, wadda aka fadada zuwa kungiyoyi 48 a karon farko, ana sa ran za ta zama mafi girma a tarihin FIFA.
Ga yadda jadawalin yake:
- Argentina
- Spain
- France
- England
- Portugal
- Brazil
- Morocco
- Netherlands
- Belgium
- Germany
- Croatia
- Italy
- Colombia
- Mexico
- Senegal
- Uruguay
- USA
- Japan
- Switzerland
- Iran
- Denmark
- Turkey
- Ecuador
- Austria
- South Korea
- Nigeria
- Australia
- Algeria
- Egypt
- Canada
- Norway
- Ukraine
- Ivory Coast
- Panama
- Poland
- Russia
- Wales
- Sweden
- Serbia
- Paraguay
- Czechia
- Hungary
- Scotland
- Tunisia
- Cameroon
- DR Congo
- Greece
- Slovakia
- Venezuela
- Uzbekistan