Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana damuwa kan yadda bangaren ilimi ke fama da karancin kudade a Najeriya.
Alausa ya ce adadin kudaden da ake warewa fannin ya yi kasa da ma’aunin da Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO ta gindaya.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta kan ware tsakanin kashi 5 zuwa 8 cikin 100 na kasafin kudin kasa ga ilimi, alhali UNESCO ta ba da shawarar a ware tsakanin kashi 15 zuwa 20 cikin 100 na kasafin kowacce shekara.
Ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda sama da dalibai miliyan biyu ke neman shiga jami’o’i a duk shekara, yayin da guraben da ake da su, ba su wuce dubu 500 ba, duk da cewa Najeriya na da jami’o’i sama da 200.
Ya qara da cewa karancin kudade na ci gaba da janyo lalacewar kayayyakin more rayuwa a makarantu, karancin kayan amfani da kuma matsalolin samun ingantaccen ilimi.
Haka kuma ya ce akwai gibi tsakanin ilimin da dalibai ke samu a jami’o’i da kuma bukatun aiki, yayin da kwararrun malamai da dalibai ke ci gaba da barin kasar domin neman ingantattun damammaki a kasashen waje.
- Gwamnatin Edo ta rufe makarantu saboda barazanar tsaro
-
An Sauya Sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur ta Kaduna Zuwa jami’ar Shehu Musa Yar’Adua
Alausa ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 65 da kafuwar Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife, Jihar Osun.
Sai dai Alausa ya ce gwamnati na kokarin inganta bangaren ilimi ta hanyar sauye-sauye da shirye-shirye irin su Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Najeriya, NELFUND, domin taimaka wa dalibai masu karamin karfi su ci gaba da karatunsu.
