’Yan bindiga sunyi garkuwa da ɗimbin ‘yan kasuwa, manoma da matafiya a wata hanya da ke kaiwa Kasuwar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Mazauna yankin sun ce maharan sun tare babbar hanyar da ke haɗa Sabon Birni da wasu al’ummomin da ke kewaye kafin su kaddamar da harin.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun iso da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Laraba a kan Babura kusan 20, sannan suka fara harbe-harbe wanda ya jefa fargaba a zukatan mutanen da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako.
- An Sauya Sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur ta Kaduna Zuwa jami’ar Shehu Musa Yar’Adua
- Ranar Demokaradiyya: Tunubu ya karrama wasu fitattun yan Kasa
- ‘Yan Sanda sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su a Katsina
“Muna zaune kusa da gada lokacin da muka ga suna tahowa a kan babura. Nan take suka fara harbi daga wurare daban-daban tare da sace matafiya, manoma da wasu mata da ke aiki a gonakin da ke kusa,” in ji shi.
Ganau ɗin ya ce aƙalla mutum 20 aka yi garkuwa da su a yayin harin.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan waɗanda aka sace, mai suna Abdurrashid, ya shaida cewa mahaifiyarsa na cikin mutanen da aka yi garkuwa da su yayin da take aiki a gona.
Ya ce mahaifinsa ba shi da lafiya kuma ba zai iya kula da iyali ba, lamarin da ya sa mahaifiyarsa ce ke ɗaukar nauyin rayuwar su.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan ba su shiga garin Sabon Birni ba, sai dai sun yi aikinsu ne a wani wuri da ake kira Mangwaron Bullun, wata mahaɗa da ke haɗa al’ummomin yankuna da dama kamar Katsira, Zakin Ganga, Maskin Wuya, Garin Dango, Garin Gardi, Garin Bage, Zududu da sauransu.
Ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka sace ba, domin iyalai da dama na ci gaba da ƙoƙarin gano inda ‘yan uwansu suke.
Duk da ƙoƙarin jin ta bakin kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, bai samu ba, domin bai amsa kiraye-kirayen wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton
Wannan sabon hari na daga cikin matsalolin rashin tsaro da ke addabar al’ummomi a Jihar Sakkwato, inda mazauna yankunan ke ci gaba da fuskantar hare-hare, garkuwa da mutane, kashe-kashe da jikkata mutane a cikin makonnin baya-bayan nan.
