NDLEA tace ta kama masu ta'ammali da miyagun kwayoyin ne karkashin shirin ta na " Operation Sharar Mafaka"

Hukumar yaƙi da sha, da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) shiyyar jihar Kano, ta samu nasarar kama mutane 73 da ake zargi tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi, a wani samamen da ta kaiwa a faɗin jihar.

Wannan bayani ya fito ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar ranar Alhamis a birnin Kano.

Muhammad-Maigatari yace ya jiyo Kwamandan hukumar na jihar, Dahiru Yahaya-Lawal, inda yake bayyana cewa an samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Yuni, ƙarƙashin wani shiri na musamman da ake kira “Operation Sharar Mafaka”.

Kwamandan ya ƙara da cewa, wannan samame na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke yi domin ganowa, tarwatsawa, da kuma murƙushe masu shaye-shaye a jihar.

“Jami’anmu sun kai samame a shahararriyar matattarar masu shaye-shaye ta Filin Mahaha, Cibiyar Matasa ta Sani Abacha (Sani Abacha Youth Centre), da kuma wasu wurare a yankin Sheka,” in ji Kwamandan.

Sanarwar tace kai sumamen ya biyo bayan samun wasu bayanan sirri game da wuraren da kuma yadda ake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, da suka hadar da Tabar wiwi da kwayoyi dake sanya maye.

Hukumar tace tana amfani ne da dabarar “tarwatsa masu laifi tare da mamaye wuraren da ake aikata su” da nufin ruguza ayyukan miyakun mutane da kuma hana dillalan ƙwayoyin samun mazauni a gari.

Duk da haka Hukumar  ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bata sahihan bayanai a kan lokaci, domin taya ta murnar kawo ƙarshen wannan annoba.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin yaki da ƙwayoyi ba zai taɓa kammala ba idan ba a toshe tushen matsalar ba.

Suna kan ra’ayin da a ce gwamnati da hukumomi a jihar Kano zasu mayar da hankali wajen samar da guraben ayyukan yi da koyar da sana’o’i, da an rage yawan matasan da ke zaman kashe wando a lunguna suna tafka ta’asa.

Irin wannan Sumame Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta dukufa akai, inda ta kama dubban matasa dake harkar daba da shaye-shaye, domin kawo karshen asarar da fadan ‘yan dabar ke haifar wa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *