Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya gargadi masu baiwa ƴan-ta’adda mafaka su kuka da kansu, domin jami’an tsaro ba za su iya samun nasara a yaƙi da matsalar tsaro ba su kaɗai ba.

Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa na kasa na shekarar 2026, wanda aka shirya a matsayin wani bangare na bikin ranar Dimokuradiyya.

Abuja: Ana cigaba da zanga-zangar tabarbarewar tsaro a Najeriya

Ya ce manyan miyagun suna ci gaba da aikata ta’addanci ne saboda suna samun tallafin abinci da sauran abin buƙata daga wasu mutane, lamarin da ke zamewa yaƙin da akeyi dasu tarnaƙi.

A cewarsa, yaƙi da ƴan bindiga da sauran miyagun laifuka na kara ta’azzara ne, sakamakon yadda ake samun masu baiwa ƴan-ta’addar kariya.

“Idan mutane suna son a samu zaman lafiya da tsaro, za’a iya samu. Amma idan ba su bayar da hadin kai ba, ba za’a samu ba, domin wasu daga cikin jama’ar gari na taka rawa wajen ci gaba da tallafawa ƴan-ta’adda,” in ji Janar Musa.

Ya kara da cewa matsalolin rashin tsaro da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga, masu garkuwa da sauran manyan laifuka, na da alaka da irin gudummuwar da wasu bara gurbi ke bayarwa.

“Akwai misalai da dama da ke nuna yadda wasu ke samar musu abinci, ruwa da kuma bayanan sirri. Wadannan abubuwa ne ke ta’azzara matsalar tsaron da taƙi-ci taƙi cinyewa” in ji shi.

Ministan ya ce kalubalen tsaro na yanzu ya sha bamban da irin na baya, inda a da ake fuskantar rikici tsakanin kasa da kasa ko jiha da jiha, kuma ana iya gane maƙiyi a fili.

“Amma a yanzu, makiyanmu na zaune tare da mu, amma ba mu san su ba,” in ji Janar Musa.

Ya jaddada cewa jami’an tsaro kadai ba za su iya kawo karshen matsalar ‘yan bindiga ba, sai idan al’umma sun bayar da cikakken goyon baya ta hanyar fallasa masu aikata laifuka da ke zaune a cikin unguwanninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *