Zaben cike-gibi a jihohi takwas: Me ya sa Ekiti ke gudanar da zabenta dabam da sauran jihohin Najeriya?

A karkashin dokar zaben Najeriya, ana gudanar da babban zaben kasar duk bayan shekara hudu, wanda ya hada da zaben shugaban kasa da na gwamnoni da kuma na ‘yan majalisun tarayya. Sai dai akwai wasu jihohi takwas da jadawalin zabensu ya sha bamban da na sauran jihohin kasar.

Jihohin sun hada da Bayelsa da Kogi da Anambra da Imo da Osun da Ondo da Ekiti. Saboda haka, zabukan gwamnoninsu ba sa gudana lokaci guda da na sauran jihohi.

 

Ta yaya aka samu wannan bambanci?

Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, jihohi na gudanar da zabukansu tare da sauran sassan kasar. Sai dai bayan zabukan shekarar 2003, wasu daga cikin ‘yan takara sun kalubalanci sakamakon zabukan a kotu.

Wasu daga cikin karar da aka shigar sun yi nasara, lamarin da ya kai ga tsige wasu gwamnoni tare da gudanar da zabukan cike-gibi a wasu jihohin. Hakan ne ya sa jadawalin zabukan jihohin ya fara bambanta da na sauran jihohi.

Yadda lamarin ya kasance a jihar Ekiti

A zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2007, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Segun Oni na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai babban abokin takararsa, Kayode Fayemi na jam’iyyar ACN, ya kalubalanci sakamakon a kotu. Bayan kusan shekara uku da Segun Oni ya yi yana mulki, kotun sauraron kararrakin zabe ta soke nasararsa a watan Oktoban 2010, tare da tabbatar da Kayode Fayemi a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Tun daga lokacin, an gudanar da zabukan gwamnan Ekiti a shekarun 2014 da 2018 da 2022, yayin da ake sa ran gudanar da sabon zaben jihar a ranar 20 ga watan Yunin 2026.

Yawan masu rajistar zabe ya karu

Hukumar INEC ta ce ta rufe aikin sabunta rajistar masu kada kuri’a a jihar Ekiti a ranar 15 ga watan Mayun 2026.

A cewar hukumar, yawan masu rajista ya karu daga mutum 987,647 a shekarar 2023 zuwa mutum 1,059,360 a shekarar 2026.

Haka kuma, adadin wadanda suka karbi katin zabensu ya karu daga mutum 958,052 a shekarar 2023 zuwa mutum 1,028,929 a shekarar 2026, wanda ke wakiltar kusan kashi 97 cikin 100 na wadanda suka yi rajista.

Da farko, an tsara fara raba katunan zaben ne daga ranar 11 ga watan Yunin 2026, amma daga bisani aka dage aikin zuwa ranar 14 ga watan Yunin 2026 bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Ado-Ekiti.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce:

“A karkashin sashe na 18(1) na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima, hukumar ta karbi bukatun maye gurbin katunan zabe da suka bace ko suka lalace guda 14,406.”

Shirye-shiryen tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da zaben jihar Ekiti, CP Abayomi Shogunle, ya ce jami’an tsaro sun kammala dukkan shirye-shiryensu domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe.

Ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin rundunar ‘yan sandan Najeriya na Facebook.

A cewarsa, za a fara jigilar kayan zabe zuwa kananan hukumomi 16 na jihar tun da karfe 6:30 na safiyar ranar zabe, kafin a kai su zuwa rumfunan kada kuri’a.

Wadanne jam’iyyu ne ke kan gaba?

Jam’iyyun siyasar da ake ganin za su fafata sosai a zaben gwamnan jihar Ekiti sun hada da jam’iyyar APC mai mulki da ADC da LP da kuma NNPP.

Ana sa ran ‘yan takarar wadannan jam’iyyu za su gwabza a zaben da za a gudanar ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *