Shahararren dan kwallon Brazil, Ronaldinho, mai shekaru 46 ya kammala komawa kungiyar Ravenna FC, da ke fafata gasar mataki na Uku na kasar Italiya.
Duk da cewa jami’an kungiyar da farko sun nuna cewa rawar da zai taka za ta takaitu ne kawai ga ayyukan talla, daga baya sun ki yin watsi da yiwuwar dan shekara 46 din ya buga wasa a fili.
A cewar jaridar Gazzetta, tsohon dan wasan wanda ya lashe Ballon d’Or an shirya za a gabatar da shi a hukumance a wani taro na musamman a Miami a ranar 23 ga Yuni.
Tambayoyi sun taso cikin sauri kan ko sa hannun Ronaldinho zai wuce ayyukan talla kawai. Mataimakin shugaban Ravenna Ariedo Braida ya ce: “Ronaldinho zai yi tallata mana kungiyar mu ne, amma ba zai buga wa Ravenna a Serie C, a kakar wasa mai kamawa ba.”
Sai dai daga bisani, Braida ya bar ƙofa a bude ga yiwuwar Ronaldinho ya bayyana a filin wasa yayin da ƙungiyar zata buga wasan ta.