Jam’iyyar APC ta samu nasara a Mazaɓar tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose

Sakamakon da aka bayyana ya nuna cewa jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 448, yayin da jam’iyyar ADC ta samu ƙuri’u 37.

Jam’iyyar PDP kuwa ta samu ƙuri’u huɗu kacal.

Wannan na nufin Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar ta samu rinjaye a mazaɓar tsohon gwamnan, wanda da haka ne ake auna mizanin nauyin ðan siyasa da tunbatsar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *