Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Abiodun Oyebanji na jam’iyyar (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti na shekarar 2026

Da take bayyana sakamakon karshe, baturiyar zaɓen Farfesa Adenike  Oladiji, ta ce Ɗan takarar Jamiyyar (PDP) Wole Oluyede, ya samu kuriu 40,543  yayin da Ɗan takarar jam’iyyar (ADC) Ambasada Dare Bajide ya zo na Uku da kuri’u 12,872

Farfesa Adenike ta cigaba da zayyano alƙalumman ƙuri’un da aka kaɗa inda Ɗan takarar jam’iyyar (APC) Abiodun Oyebanji ya samu kuri’u 319,224, inda anan ne ta ayyana shi a matsayin wanda yayi nasara.

Zaɓaɓɓen Gwamnan zai zarce ne a wa’adin zangon mulki na shekara Huɗu, a jihar ta Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *