Bayan wata ziyara da sabon shugaban ƙasar Benin, Romuald Wadagni, ya kai Nijar a farkon wannan wata, an gudanar da jerin tattaunawa a birnin Cotonou a ƙarshen mako, domin hanzarta dawo da kyakkyawar dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu
An samu rashin jituwa tsakanin Nijar da Benin tun bayan da sojoji suka karɓi mulki a Nijar a watan Yulin 2023, inda suka rufe iyakar ƙasar da Benin tare da takaita harkokin kasuwanci.
Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta zargi Benin da karɓar baƙuncin sansanonin sojojin Faransa, taimakawa ƙoƙarin kawo cikas ga sabbin shugabannin Nijar, da kuma zama wata hanya da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ke amfani da ita wajen kai hare-hare a ƙasar.
- FIFA za ta biya Alƙalin wasan da Amurka ta hana shiga ƙasar ta Albashin sa
- Afirka ta samu nasarar farko a gasar cin kofin duniya na 2026
- Senegal: Kasashen ECOWAS sun bude taro kan makamashi
Bayan juyin mulkin, gwamnatin Nijar ta katse kusancinta da Faransa, wadda ita ce tsohuwar uwargijiyar ta, kuma babban abokiyar hulɗar ta a baya.
Kamar sauran ƙasashen yankin, Nijar da Benin suna fuskantar matsalar hare-haren masu iƙirarin jihadi da ta’addanci.
Sai dai ziyarar da Romuald Wadagni ya kai Nijar a ranar 2 ga Yuni ta sake farfaɗo da ƙoƙarin dawo da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
A ranar Asabar, sabbin kwamitocin haɗin gwiwa da aka kafa sun ci gaba da tattaunawa kan sake buɗe iyakar da ke tsakanin ƙasashen da kuma warware rikicin da ya janyo tsaikon dangantaka.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan harkokin tsaro da kariya, diflomasiyya da harkokin shari’a, da kuma tattalin arziki.
Wani wakili da ya halarci taron ya bayyana cewa sake buɗe iyakar tsakanin ƙasashen “al’amari ne da aka riga aka amince da shi.”
An kuma tsara ci gaba da tattaunawar a ranar Lahadi domin ƙarfafa fahimtar juna da cimma matsaya kan sauran batutuwan da suka rage, da suka jiɓanci tsaro da makomar Nijar.