Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu kwalejojin horas da ma’aikatan lafiya guda biyu da ke aiki ba bisa ka’ida ba a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar.

Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta ce ta ɗauki matakin rufe IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke yankin Dakata Industrial Area, Bela Road, Tsamiyar Gare, kan titin Mai Sikeli.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Lafiya, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar, an gano cewa cibiyoyin biyu ba su cika ƙa’idoji da matakan da ake buƙata wajen kafa da gudanar da kwalejojin horas da lafiya ba a jihar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa bincike ya gano rashin samun ingantaccen amincewa daga hukumomin da suka dace, ƙarancin ƙwararrun malamai, rashin wadatattun kayan koyarwa da kuma gazawar cibiyoyin wajen bin ƙa’idojin da suka shafi koyar da harkokin lafiya.

Gwamnatin Kano ta ce rufe cibiyoyin wani mataki ne na kare ɗalibai, iyaye da kuma jama’a daga cibiyoyin da ka iya rage ingancin horas da ma’aikatan lafiya, tare da gargadin sauran masu gudanar da irin waɗannan makarantu da su tabbatar da bin dukkan ƙa’idoji da dokokin da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *