Hukumomin makarantar sun ce duka ko cin zarafi, baya cikin tsarin su

Mahukuntan Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara (Kwara Poly) sun sanar da dakatar da wani malami daga aiki, bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, inda yake yiwa wasu dalibai bulala.

A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta kwalejin, Halimat Garba, ta fitar, ta bayyana cewa mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Kwara ba ne.

Daliban na karatu ne a fannin share fagen shiga jami’a (IJMB), waɗanda rahotanni suka nuna sun isa a makare wajen rubuta jarabawar.

Kwalejin ta sanar da dakatar da malamin daga gudanar da aikinsa nan take, har zuwa lokacin da za’a kammala binciken da ake yi kan lamarin.

“Ko da yake har yanzu ba a tantance dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki ba, muna son jaddada cewa hanyar da aka bi ba ta dace ba, domin Kwalejin na adawa da duk wani nau’i na tashin hankali ko hukuncin jiki a matsayin hanyar ladabtarwa,” in ji sanarwar.

Haka kuma, mahukuntan sun ce sun lura da damuwar da jama’a da masu ruwa da tsaki suka nuna dangane da bidiyon da ya bazu, tare da tabbatar da cewa ana ɗaukar batun da matuƙar muhimmanci.

Sun kuma sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da kare martaba da ƙimar da cibiyar ta yi suna da su, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda iyaye da dalibai da kuma sauran jama’a suka yi Allah-wadai da abin da ya faru.

Mutane da dama sun soki amfani da hukuncin duka a muhallin ilimi, suna masu cewa hakan ya yi tsauri kuma bai dace da tsarin koyarwar zamani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *