Gwamnatin Jihar Sokoto ta ƙara ƙaimi wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da yara tare da inganta rigakafin yara, ta hanyar wayar da kan shugabannin al’umma a dukkanin gundumomi 244 na jihar domin su jagoranci yaɗa saƙonnin kiwon lafiya a matakin ƙasa.
An bayyana wannan shiri ne a yayin wani taron kwana biyu na wayar da kai da horaswa da Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Sokoto ta shirya wa Kwamitocin Raya Gundumomi (WDCs) tare da tallafin Tarayyar Turai ƙarƙashin shirin SARAH da kuma Community Engagement and Accountability (CEA).
Daraktan Wayar da Kai da Tattara Ra’ayin Jama’a na hukumar, Dahiru Gada, ya ce manufar shirin ita ce bai wa wakilan al’umma cikakken fahimtar shirye-shiryen domin su koma yankunansu su ilmantar da jama’a kan ayyukan kiwon lafiya da muhimmancin amfani da su, musamman kula da mata masu juna biyu da haihuwa a cibiyoyin lafiya.
- Ministar Abuja ta nesanta kanta daga zargin naɗin mataimaka bakwai
- Mutum ɗaya ya jikkata yayin da wani abin fashewa ya tashi a Legas
Ya bayyana cewa shugabannin al’umma na taka muhimmiyar rawa wajen kawar da rashin fahimta da ƙarfafa amincewar jama’a da harkokin lafiya, yana mai cewa karɓar kulawar masu juna biyu da haihuwa ƙarƙashin kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen rage mace-macen mata da yara.
Shi ma Shugaban Kwamitocin Raya Gundumomi na Jihar Sokoto, Bala Gadanga, ya ce nasarar shirin ta dogara ne da samun cikakken haɗin kan al’umma, yana mai bayyana cewa mahalarta taron za su koma yankunansu domin ci gaba da wayar da kan jama’a, bibiyar yaran da suka rasa rigakafi da kuma tura mata masu juna biyu zuwa cibiyoyin lafiya domin samun kulawar da ta dace.