Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Ahmed Muhammed Sanusi, ya gana da shugabannin Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta yankin Abuja domin tattauna matsalolin da ke addabar makiyaya da kuma hanyoyin tabbatar da zaman lafiya.
A wata ganawa da aka yi a hedikwatar rundunar da ke Garki a ranar Litinin 22 ga watan Yunin 2026, shugaban shiyyar Arewa ta Tsakiya na ƙungiyar, Alhaji Gidado Idris Bebeji, ya jagoranci tawagar zuwa ziyarar girmamawa ga kwamishinan.
- Tinubu ya tura Kudirin ’Yan Sandan Jihohi ga Majalisa
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta rufe shari’arta kan Nasir El-Rufa’i
Shugabannin Kungiyar sun bayyana damuwarsu kan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma, da kuma sabani da wasu Kungiyoyin sa-kai na tsaro.
Sun kuma koka kan hare-haren masu garkuwa da mutane da masu satar shanu, da zargin guba ga dabbobi daga wasu manoma, da kuma yadda gonaki da gine-ginen gidaje ke mamaye tsofaffin hanyoyin kiwo, lamarin da suka ce na kara haddasa rashin jituwar makiyaya da mazauna yankuna da kuma manoma.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce rundunar za ta yi gaggawar magance matsalolin da ke karkashin ikonta bisa tanadin doka, yayin da ya bayyana cewa za a miƙa batutuwan da suka wuce ikon rundunar ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakan da suka dace.
Ya kuma yi alkawarin tattaunawa da manoma da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin warware sabanin da ke tsakaninsu da kuma karfafa zaman lafiya.
Ahmed Muhammed Sanusi ya jaddada muhimmancin fahimtar juna da mutunta juna tsakanin makiyaya, manoma da al’ummomin da suke zaune tare domin kauce wa rikice-rikice.
Har ila yau, ya nuna damuwa kan yadda ake bai wa kananan yara aikin kiwon shanu, da kuma yin kiwo da daddare ko a cikin birane, yana mai gargadin makiyaya da su guji kiwo a manyan tituna da tsakiyar birane saboda haɗarin da hakan ke jefa jama’a da dabbobin kansu.
Ya kuma shawarci makiyaya su takaita kiwo zuwa wajen garuruwa tare da kauce wa shiga gonaki domin hana lalata amfanin gona da kuma kauce wa rikice-rikice.
Kwamishinan ya yi gargadi game da ɗaukar doka a hannu idan rikici ya taso, tare da kira ga mambobin ƙungiyar da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani mutum ko motsi da suke zargin baƙon abu ne a yankunansu.
Ya ce duk wanda ya ɓoye masu aikata laifuka ko ya ƙi sanar da hukumomi game da su na iya fuskantar hukunci a matsayin mai taimaka wa masu laifi.
A nasa bangaren, shugabannin Miyetti Allah sun gode wa rundunar bisa karɓar baƙuncinsu, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin inganta zaman lafiya da tsaro a Babban Birnin Tarayya Abuja.