Ƙasashen Amurka da Iran sun ci gaba da fitar da bayanai masu saɓani, kan batun sa ido kan shirin nukiliyar Iran, yayin da masu tattaunawa ke ƙoƙarin cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin wa’adin kwanaki 60 da aka tsara
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa Iran ba za ta samu damar karɓar kuɗin haraji ko kuɗin wucewa daga jiragen ruwa a mashigin Hormuz ba idan aka cimma yarjejeniya ta ƙarshe
Sai dai Iran ta ƙaryata ikirarin Amurka cewa za ta sake bai wa masu sa ido kan makamashin nukiliya damar shiga ƙasar
- Najeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar yaƙi da ta’addanci
- Me ya sa Keir Starmer ya yi murabus daga mukamin Firayim Ministan Birtaniya?
- Hormuz: Iran da Amurka zasu koma teburin sulhu
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Tehran ta amince da mafi girman matakin sa ido da bincike kan shirinta na nukiliya
A nasa ɓangaren, Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa shirin makamai masu linzami (ballistic missiles) na Iran ba ya cikin abubuwan da ake tattaunawa da Amurka a kai
A wani bangare kuma, Isra’ila da Lebanon sun fara zagaye na biyar na tattaunawar da Amurka ke shiga tsakani
Sai dai wakilin Isra’ila ya bayyana tattaunawar a matsayin “wani yanayi mai cike da rikice-rikice da matsaloli”, yana nuna cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale wajen cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu
