Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya himmatu wajen bunƙasa samar da gidaje a faɗin ƙasar nan, tare da cika burin samar da gidaje dubu 100 a wa’adin farko na gwamnatin.
Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqha Darma ne ya fadi hakan yayin da yake jawabi yayin rabon wasu gidaje ga wadanda suka ci gajiyar shirin da Gwamnatin Tarayya da Bankin Lamunin Gidaje FMBN, suka shirya,.
Rabe Darma ya bayyana cewa yawan kuɗaɗen haya da ‘yan Najeriya ke kashewa, musamman a biranen Abuja da Legas, ya sa samar da gidaje masu araha ya zama wajibi ga gwamnati.
Ya kuma yi alƙawarin cewa matsalolin jinkirin rabon gidaje da wasu masu cin gajiyar shirin suka fuskanta a baya ba za su sake faruwa ba, yana mai cewa lokaci ya yi na aiwatar da ayyuka maimakon yawan alkawura.
- Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Sababbin Jakadu Huɗu Takardun Shaidar Diflomasiyya.
-
Gwamnatin Tarayya za ta baiwa jihohi Kuɗaɗe kan barazanar Cututtuka
-
Gwamnatin tarayya zata fara biyan kananan ’yan kwangila bashi
A nasa ɓangaren, Shugaban Babban Bankin Lamunin Gidaje na Najeriya (FMBN), Shehu Osidi, ya ce an warware matsalolin da suka dabaibaye aikin, tare da tabbatar da cewa duk waɗanda aka tantance a matsayin masu cin gajiyar shirin za su samu gidajensu.
Ya ce tsarin “Haya zuwa Mallaka” (Rent-to-Own) na bai wa masu neman gida damar shiga gidajensu ba tare da biyan kuɗin kaso na farko ba, inda suke biyan kuɗin haya a hankali har sai sun mallaki gidan gaba ɗaya.
Shi ma wakilin kamfanin Brains and Hammers, Tanks Adamu, ya ce gidajen da aka gina sun haɗa da gidaje masu ɗakuna biyu da uku tare da kayayyakin more rayuwa na zamani.
Da yake magana a madadin masu cin gajiyar shirin, Sanusi Dansoro ya yabawa Gwamnatin Tarayya da FMBN bisa ba su damar mallakar gidaje, yana mai cewa haɗin gwiwar gwamnati, cibiyoyin kuɗi da masu gina gidaje na samar da sakamako mai anfani ga al’umma.
