Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya kai ziyara Angwan Rukuba da ke Jos, domin jajantawa al’umma bayan harin bindiga da aka kai a Kasuwar Gari Ya Waye, ya lashi takobin binciko da hukunta waɗanda suka aikata aika-aikar.
Yayin ziyarar, Mutfwang ya bayyana alhininsa ga iyalan da suka rasa danginsu da wadanda aka raunata.
Ya tabbatar wa al’umma cewa kowane iyali zai samu damar gudanar da jana’iza yadda ya kamata ga ‘ƴan uwansu da aka kashe.
Ya ce gwamnati za ta dauki dukkan nauyin kudaden da ake buƙata.
Ga waɗanda suka samu raunuka nauyin yi musu magani zai kasance a wuyan gwamnati, inji Mutfwang.
Gwamnan ya ja kunne kan cewa hukumomin tsaro za su kamo duk wanda aka samu yana wallafa kalaman tunzuri ko rura wutar rikici a kafafen sada zumunta.
Ita ma Kungiyar Cigaban Jasawa (JCDA) Allah wadai ta yi da harin, wanda ta kira da yunƙurin raba kan al’umma.
Wata sanarwa da Sakatarenta Ambassada Sani Suleiman ya fitar ta ce al’ummar Jos na buƙatar addu’o’in dukkanin jama’a, domin neman tsari daga makircin maƙiya cigaban jihar.
Ambassada Sani ya bayyana harin a matsayin “aikin dabbanci” da nufin ruguza zaman lafiyar jihar.
Daga nan ya bukaci a binciki bidiyon wani dan ƙasar waje da aka gani yana kalaman tunzuri a wurin da abin ya faru.
Ya kuma buƙaci matasa su daina tare hanya ko kai wa matafiya hari, yana mai cewa hakan yana kara dagula matsalar ne maimakon magance ta.
© Blueprint Hausa Radio Online 2026