Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Alhaji Ibrahim Musa Gusau, ya sake jaddada aniyar Hukumar na bunkasa ƙwallon ƙafa daga matakin ƙasa zuwa Jihohi da kuma samar da hanyoyin samun ilimin horarwa cikin sauki.
Gusau, ya bayyana hakanne bayan kammala bitar sabunta Ilimin Lasisin CAF B da hukumar ta shirya a ranar Laraba da yamma.
Da yake jawabi a wajen taron rufe bitar, Gusau ya gode wa mahalarta da masu ruwa da tsaki bisa jajircewarsu ga shirin.
Ya ƙara da cewa harkar ƙwallon ƙafa, ciki har da ilimin horarwa, ta samu gagarumin ci gaba tun bayan da gwamnatinsa ta hau mulki shekaru kaɗan da suka wuce.
-
Scotland 0-3 Brazil: Vinicius ya kafa tarihi
-
Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026: Afirka ta Kudu, Morocco sun kai zagaye na 32
“Lokacin da muka zo, lamarin bai kasance mai kyau ba dangane da ilimin horarwa. Na yi imani dukanku za ku iya shaida cewa an samu ci gaba sosai a wannan fanni, tare da kwasa-kwasan da muka yi da yawa da kuma dawowar ƙasarmu zuwa yarjejeniyar Lasisin CAF A,” in ji shi.
Gusau ya tabbatar cewa hukumar NFF za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau da ake buƙata domin masu horarwa da ‘yan wasa su bunƙasa.
Jimillar masu horarwa 50 suka halarci atisayen kuma aka sabunta musu ilimin horarwa na kwanaki huɗu, wanda ya fara ranar Lahadi.
Taron rufe bitar ya samu halartar Babban Sakataren NFF, Dr. Mohammed Sanusi MON (wanda shi ma ɗaya ne daga cikin malamai); Daraktan Fasaha na NFF, Koci Augustine Eguavoen (wanda shi ma malami ne); Shugaban Sashen Ilimin Horarwa na NFF, Dr. Terry Eguaoje; Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na NFF, Dr. Ademola Olajire; Koci Abdulrafiu Yusuf da; Shugaban Ƙungiyar Masu Horar da Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Koci Ladan Bosso.
