Wata Babbar Kotu Tarayya da ke Abuja ta soke sammacin da ta bayar ranar 26 ga watan Maris na kamo Barista Kabiru Tanimu Turaki, shugaban wani tsagi na jam’iyyar PDP.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Peter Kekemeke ne ya soke sammacin ranar Laraba yayin da yake yanke hukunci a kan wata bukata ta baka da lauyan Turaki, Chris Uche (SAN), ya gabatar bayan bayyanar jigon na PDP a gaban kotun.
Lokacin da aka kira karar, Uche ya nemi afuwar kotun saboda rashin halartarsa a zaman da ya gabata.
Uche, wanda ya yi ikirarin cewa ba ya kasar, ya ce ya dawo ne ranar Laraba da sassafe kuma ya nufi kotun kai tsaye.
Ya kuma nemi afuwa a madadin wanda yake karewa, wanda ya ce Babban Lauya ne (SAN) mai girmama kotu matuka.
Ya ce rashin halartar Turaki a zaman da ya gabata ba da gangan ba ne ko don raini, inda ya kara da cewa ba shi da niyyar nuna rashin kunya ga kotu.
A Shirye Yake
Uche ya kara da cewa har ila yau Turaki a shirye yake ya bayyana matsayinsa game da tuhumar da ake yi mishi a gaban kotun.
Da yake mayar da martani, lauyan masu shigar da kara, Usman Rabiu, ya ce ba ya adawa da bukatun Lauya Uche.
“Tunda shi (Turaki) yana nan, ba ma adawa da a karanta masa laifukan nasa a yau”, inji Lauya Usman.
A yayin yanke hukunci, Alkali Kekemeke ya lura cewa wanda ake tuhumar ya zo kotun da kansa kafin ma a aiwatar da sammacin kama shi.
Alkalin ya kuma lura cewa lauyansa ya nemi afuwa game da rashin halartarsa, ko da yake dalilin rashin zuwan nasa bai fito fili ba daga bayanin da Uche ya yi.
Duk da haka, ya zabi ya yafe wa wanda ake tuhumar tare da soke sammacin.
Bukatar Tanimu Turaki
Mai Shari’a Kekemeke ya ce tun da an tsara ranar Laraba ne domin sauraron bukatar da wanda ake tuhumar ya shigar ta dakatar da sammacin kama shi, bai dace a ci gaba da karanta mishi tuhume-tuhumen ba.
Don haka alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Afrilu domin karanta wa Turaki tuhumar da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya shigar a kansa.
Ana dai zargin Shugaban Tsagin na PDP ne da Sharara karya a wasu bayanai da ya yi wa ’yan sanda a 2022.
