Kaan Ayhan ya zura ƙwallon da ta baiwa Turkiyya nasara yayinda ake dab da tashiwa a wasa tsakaninta da Amurka.

Turkiyya ta hana Amurka kammala wasannin rukunin D na Kofin Duniya ba tare da an ci ta ba, inda ta samu nasara mai ban sha’awa da ci 3-2 a Los Angeles.

Turkiyya wadda aka riga aka fitar da ita ɗaga gasar bayan shan kashi biyu a jere a hannun Australia da Paraguay ta zura ƙwallonne a minti na 98.

Amurka, wadda ta riga ta tabbatar da zuwa zagaye na 32 a matsayin shugabar rukunin na D, zata, ƙara ne da Bosnia-Herzegovina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *