Lionel Messi ya sake kafa sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya ta 2026 yayin da ya zura ƙwallo a bugun tazara a minti na 80 inda ya taimaka wa Argentina ta doke Jordan da ci 3-1 a wasan rukuni na J a safiyar ranar Lahadi, a filin wasa na Dallas. 

Messi ya zama ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallo a wasanni bakwai na Kofin Duniya a jere, sannan kuma ya zura ƙwallo ta shida a gasar bana inda ya ƙara baiwa abokan takararsa tazara don lashe Takalmin Zinare.

Messi, wanda ya yi murnar cika shekara 39 a farkon wannan makon, shi ne dan ƙasar Argentina na biyu da ya buga wasan Kofin Duniya yana da shekara 39, bayan Angel Labruna a 1958.

Argentina za ta fafata ne da Cape Verde a wasan gaba na zagayen ƙasashe 32 ranar Jumma’a 3 ga watan Yulin 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *