Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce Kyaututtukan Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i na Ƙasa na shekarar 2026 sun nuna ƙudirin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na mayar da ƙanana da matsakaitan sana’o’i ginshiƙin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya ƙarƙashin tsarin (Renewed Hope Agenda).
Ministan ya bayyana hakan ne bayan bikin karrama fitattun ‘yan kasuwa da aka gudanar a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Asabar.
Ya ce karramawar da aka yi wa fitattun masu sana’o’i na nuna ƙudirin Gwamnatin Tarayya na samar da yanayi mai kyau da zai baiwa kasuwanci damar bunƙasa, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
- An karrama Ministan Yaɗa Labarai kan gudunmawarsa wajen bunƙasa ƙananan da matsakaitan sana’o’i da samar da ayyukan yi
- ’Yan sanda sun kama wasu ’yan’uwa biyu kan zargin yi wa ƙaramar yarinya fyade
Ministan yace rabon tallafin Naira biliyan ɗaya ga ƙananan ƴan kasuwa zai ƙarfafa ƙananan sana’o’i tare da bunƙasa tattalin arziƙi.
Ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin su yi amfani da shi wajen faɗaɗa kasuwancinsu, da taimaka wa sauran masu tasowa da kuma samar da ayyukan yi.
Mohammed ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da haɗa kai da jihohi da kamfanoni masu zaman kansu, domin bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin ƙasa.