Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio dana Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta SERAP ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da su gaggauta mika zarge-zargen karkatar da kudaden ayyukan mazabu da yawansu ya kai naira biliyan 6.3 ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin gudanar da bincike da daukar matakin shari’a.

SERAP ta mika wannan buƙata cikin wata sanarwa data fitar.

Ta ce ya kamata shugabannin majalisun biyu su tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kudaden gwamnati an gurfanar da shi a gaban kotu idan akwai isassun hujjoji

Ta kuma buƙaci a ƙwato duk wasu kudaden ayyukan mazabu ko wasu kuɗaɗen gwamnati da aka karkatar ko kuma ba a iya tantance inda suka shiga ba, tare da mayar da su cikin asusun gwamnati.

Haka zalika, ƙungiyar ta yi kira da a bayyana sunayen ‘yan kwangila da kamfanonin da suka karɓi kuɗaɗen ayyukan mazabu amma suka gaza aiwatar da ayyukan, ciki har da sunayen masu hannun jari da kuma masu cin gajiyar kamfanonin.

A cewar SERAP, wadannan zarge-zarge suna kunshe ne a cikin rahoton shekara ta 2022 na Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya (Auditor-General of the Federation), wanda aka wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025.

Sanaewar ta ce zargin ɓacewar sama da naira biliyan 6.3 na kuɗaɗen ayyukan mazaɓu na nuna yiwuwar cin amanar dukiyar jama’a, tare da saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma ƙa’idojin kasa da kasa.

SERAP ta jaddada cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa na da alhakin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kudaden ayyukan mazaɓu, tana mai cewa majalisar za ta iya cika wannan nauyi ne kawai idan ta nuna jagoranci ta hanyar binciken zarge-zargen da suka shafi ayyukan da ‘yan majalisa suka amince da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *