Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Adamawa ta ta kama mutane 583 da ake zargi da hannu a laifukan miyagun ƙwayoyi, yayin da kotu ta yanke wa mutum 270 hukunci cikin shekara guda

Kwamandan NDLEA na Jihar Adamawa, Aliyu Abubakar, ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a Yola a ƙarshen mako, inda ya ce hukumar ta kuma kwace sama da tan biyar na miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira

A cewarsa, miyagun ƙwayoyin da aka kwace sun haɗa da Tramadol, Diazepam da Codeine masu nauyin kilogram 2,451.684, da kuma tabar wiwi (Cannabis) mai nauyin kilogram 2,925.089

Aliyu ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tare da yin aiki kafada-da-kafada da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar ta hanyar sabbin dabaru da matakan kariya

Ya ce taken bikin bana ya nuna irin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta wajen yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi, ba a Jihar Adamawa kaɗai ba, har ma a faɗin Najeriya baki ɗaya

Ya kuma bayyana wasu nasarorin da hukumar ta samu, ciki har da horas da ɗaliban makarantun sakandare maza 36,082 da mata 28,334 kan hanyoyin kare kai daga shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Bugu da ƙari, Aliyu ya ce hukumar ta yi nasarar jinya da sake dawo da mutane sama da 111 cikin al’umma bayan sun daina shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda Kwamishinan Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hon. Aloysious Baba Doke ya wakilta, ya yaba wa hukumar NDLEA bisa jajircewarta wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya a duk lokacin da ake buƙata domin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da suka shafe su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *