Sojojin Amurka sun sake kai hare-hare kan wasu muhimman wurare da dama a cikin ƙasar Iran bisa zargin Iran da kai hari kan wani ruwan kasuwanci a yankin tekun da ke kusa da mashigin Hormuz.
Har ila yau, shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sada zumunta, inda ya zargi Iran da sake keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Trump ya yi barazanar cewa, “akwai yuwuwar wata rana, ba za mu ci gaba da aiki da hankali ba,” kuma za mu sake daukar matakan soji sakamakon yadda aka tilasta mana. “Idan hakan ya faru, Iran ba za ta ci gaba da wanzuwa ba!”
- Majalisar Dattawan Amurka ta Amince da Ƙudurin neman Trump ya dakatar da yaƙi da Iran
- Shugaban Hezbollah ya yi watsi da yarjejeniyar tsaro tsakanin Lebanon da Isra’ila
- Israila da Lebanon sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta
A nata bangaren, a jiya Lahadi 28 ga wata, rundunar juyin juya hali ta Iran, wato IRGC, ta sanar da cewa, sojojin ruwa da na sama na rundunar sun yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda suka lalata wasu muhimman kayayyaki na sojojin Amurka da ke wasu sassa guda 8, ciki har da sansanin sojin saman Ali Al Salem da ke kasar Kuwait, da kuma rundunar sojin ruwa ta biyar ta Amurka da ke Bahrain, a matsayin martani mai tsauri ga hare-haren da Amurka ta kai wa Iran a ‘yan kwanakin nan
Sanarwar ta kuma ce, bangaren Amurka ya kai hari kan wasu tashoshi 5 na hangen nesa dake gabar tekun Iran, bisa hujjar cewa sojojin ruwan rundunar IRGC sun “dakatar da wani jirgin ruwa da ya saɓa ka’ida.”
A cewar sanarwar, bisa yarjejeniyar fahimtar juna da ke tsakanin Iran da Amurka, ikon kula da harkokin zirga-zirga a mashigin Hormuz na hannun Iran, kuma daga yanzu za a kara daukar tsauraran matakai kan jiragen ruwa “masu saba ka’ida”.
Ɓangaren sojojin Kuwait shi ma ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce an riga an fara aiki da tsarin tsaron sararin sama na kasar, don tunkarar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na “makiya”.
A na ta bangare, ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Bahrain ta sanar a shafukan sada zumunta cewa, an riga an buga kararrawar gargadin hare hare ta sama a kasar, kuma ana bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su nufi wurare masu tsaro dake kusa da su