Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kirista a Najeriya.

Trump ya yi wannan iƙirari ne ranar Jumma’a a wani taron da aka yi a Washington, inda ya yi magana kan ayyukan tsaron gwamnatin sa da ƙoƙarin yaki da ta’addanci a sassa daban-daban na duniya.

A cewar Trump, shiga tsakani da Amurka ta yi a Najeriya ya taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hare-haren da ake zargi an yi niyya ne ga al’ummomin Kirista, musamman a yankunan da rikici da ayyukan ‘yan ta’adda suka shafa.

“Kamar yadda kuka sani, kwanan nan mun kai hari Najeriya kuma mun kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa al’ummar Kirista,” in ji shi.

Dan Jam’iyyar Republican ya ce halin da Najeriya ke ciki kafin a kai harin yana da tsanani, inda ya ce an kashe mutane marasa laifi da yawa a munanan hare-hare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *