Sabon Kocin Man City, Enzo Maresca

Enzo Maresca ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku don maye gurbin Pep Guardiola a filin wasa na Etihad.

Har wayau, City za ta biya Chelsea fiye da fam miliyan 17 a matsayin diyya na wani ɓangare na yarjejeniyar, a cewar Sky ta Italiya.

A baya can, Maresca mai shekaru 46, ya yi aiki a matsayin mataimakin Guardiola a lokacin da Man City ta lashe kofuna uku a kakar 2023, sannan kuma ya jagoranci Ƙungiyar zuwa lashe gasar Firimiya 2 a kakar 2020/21 guda ɗaya da ya yi a matsayin koci.

Da yake magana bayan naɗin nasa, Maresca ya ce: “Manchester City ƙungiya ce da na sani sosai kuma samun damar horar da wannan ƙungiya dama ce mai ban sha’awa a gare ni.

“Wannan zai zama karo na uku da nake nan. Na san wannan ƙungiyar, na san buƙatunta kuma na san abin da ake tsammani.

“Ina son mu yi nasara, mu buga ƙwallo mai kyau kuma mu ji daɗin wakiltar Manchester City.”

Maresca, ya jagoranci Blues zuwa lashe gasar UEFA Conference League da Kofin Duniya na ƙungiyoyi a kakar sa guda ɗaya kawai da ya yi a matsayin koci, kuma ya bar ƙungiyar yana matsayi na 5 a teburin gasar Firimiya, sama da inda suka ƙare a matsayi na 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *