Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa kwamandoji 76 na ƙungiyar ISWAP sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Mai magana da yawun rundunar Operation hadin kai, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau ranar Litinin, a cewarsa, matakin ya biyo bayan ƙarin hare-haren sama da na ƙasa da sojoji ke kai wa sansanonin ‘yan ta’adda, tare da samun sahihan bayanan sirri da suka ƙara matsa wa ƙungiyar lamba sanarwar ta ce matsin lambar da sojoji ke ci gaba da yi, ya tilasta wa mayaƙan ISWAP barin maboyarsu tare da miƙa wuya.
-
Shugaban adawar jamhuriyar dimokuraɗiyar congo ya ce an hana shi fita daga ƙasar.
-
HRW: Bangarorin da ke yaƙi a Mali na cin zarafin Bil Adama
Kungiyar ta ƙara da cewa wasu daga cikin manyan jagororin ISWAP na cikin waɗanda suka miƙa wuya, kuma a halin yanzu suna wani wuri mai tsaro inda ake tantance su, tare da yi musu tambayoyi da kuma kammala sauran matakan da suka dace bisa ƙa’idojin aikin soja.
Rundunar ta bayyana cewa wannan ci gaba na nuna tasirin hare-haren da ake ci gaba da kai wa ƙungiyoyin ta’addanci domin tarwatsa tsarin jagorancinsu, lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki, da kuma taƙaita zirga-zirgarsu, sojojin sun kuma ce miƙa wuyan mayaƙan, ciki har da waɗanda suka zo tare da iyalansu alama ce da ke nuna cewa ƙarfin faɗa da ƙwarin gwiwar ƙungiyar ISWAP na ci gaba da raguwa.