Mutane biyar sun rasa rayukansu bayan wani harin bindiga da ya afku a wata cibiyar kula da matasa a garin Stade da ke arewacin Jamus a ranar Litinin 29/6/2026.
‘Yan sanda sun sanar da cewa sun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wanda ake kyautata zaton shi ne ya kai harin.
Mai magana da yawun ‘yan sanda ya ce har yanzu ba a gano dalilin harin ba.
- Tehran ta musanta shirin tattaunawa da Amurka da Trump yace za a yi
- Shugaban adawar jamhuriyar dimokuraɗiyar congo ya ce an hana shi fita daga ƙasar
- HRW: Bangarorin da ke yaƙi a Mali na cin zarafin Bil Adama
Garin Stade na kusa da birnin tashar jiragen ruwa na Hamburg.
Binciken farko ya nuna cewa harin ya faru ne a wata cibiyar kula da jin daɗin matasa da ke garin Stade a yammacin Hamburg, wanda ke da yawan jama’a kusan 50,000.
Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda sun killace yankin da harin ya afku, yayin da ƙwararrun masu binciken shaidu da jami’an tsaro suka bazama domin gudanar da bincike.
Da farko hukumomi sun gargadi mazauna yankin da su guji zuwa wurin, amma daga baya suka sanar da cewa babu wata barazana ga sauran jama’a.
Hare-haren bindiga masu kashe jama’a da yawa ba safai suke faruwa a Jamus ba, musamman idan aka kwatanta da Amurka.
Sai dai ƙasar ta taɓa fuskantar wasu manyan hare-hare makamantan wannan.
A shekarar 2023, wani ɗan bindiga ya kashe mutum shida a wani wurin ibadar Jehovah’s Witnesses a Hamburg kafin daga bisani ya kashe kansa.
Haka kuma a shekarar 2016, wani matashi ɗan asalin Jamus mai jinin Iran mai shekara 18 ya kashe akalla mutum tara a birnin Munich, bayan ya kamu da sha’awar hare-haren kashe jama’a.