Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) ta bayyana cewa wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna jami’anta suna magana da Peter Obi an yi masa sauyi da nufin yaudarar jama’a da haifar da fahimta mara kyau.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, rundunar ta ce an ƙara hotunan kamfen na siyasa da rubuce-rubuce a bidiyon domin nuna kamar akwai hulɗar siyasa tsakanin jami’an ‘yan sanda da Obi, alhali hakan ba gaskiya ba ne.
Rundunar ta bayyana cewa asalin abin da ya faru ya auku ne a shekarar 2024 lokacin da aka samu kiran gaggawa game da rikici da tashin hankali da ya taso sakamakon saɓanin shugabanci a hedikwatar jam’iyyar Labour Party da ke Utako, a Abuja.
- Najeriya ta cika shekara 20 ba tare da ƙidayar Jama’a ba
- Yaran Borno da aka sace: ‘Ba mu san ko yaranmu suna raye ba’- Iyaye
- Majalisa ta gaza wajen dakatar da Gwamnati kan yawaitar cin bashi – Sarki Sanusi
Bayan kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda sun garzaya zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya da tabbatar da doka da oda.
A yayin wannan aikin ne Peter Obi ya kasance a wurin kuma ya yi ɗan bayani ga jami’an domin fayyace halin da ake ciki dangane da rikicin jam’iyyar.
Rundunar ta ce wannan magana ta faru ne ne kawai a matsayin wani ɓangare na aikin ‘yan sanda, ba tare da wata alaka da siyasa ba.
Kwamishinan ‘Yan Sandan CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan asalin bidiyon domin gano masu yaɗa shi tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da hannu.
Rundunar ta jaddada cewa ta kasance cibiyar da ba ta da alaƙa da siyasa, kuma tana ci gaba da gudanar da aikinta na tabbatar da tsaro da bin doka a cikin al’umma.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba su da tushe, tare da tabbatar da sahihancin labarai daga hukumomin da suka dace kafin su ya ɗ a su a kafafen sada zumunta.