An kama ɗan sanda da wasu mutum biyu kan zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyade a Jihar Neja.
Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Neja, Hajiya Hadiza Kuta, ta tabbatar da kama wani jami’in ɗan sanda da wasu mutum biyu bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyade.
Ta ce iyayen yarinyar ne suka kai ƙarar lamarin ga ma’aikatar bayan sun ce ƙoƙarinsu na neman adalci ya ci tura, lamarin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.
-
EFCC ta ƙwato sama da Naira biliyan 38 a binciken kuɗaɗen gyaran matatun mai
-
Ba mu karbi Kuɗi a hannun Obi ba – ‘Yan Sanda
Kwamishiniyar ta bayyana cewa ana zargin mutanen uku sun yi amfani da damar da suka samu bayan sun sayi kaji daga hannun yarinyar, tare da yin zargin cewa an yi ƙoƙarin karkatar da hankali daga shari’ar ta hanyar zargin yarinyar da satar dabbobin gida.
Hajiya Hadiza ta nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren fyade da suka shafi yara, inda ta yi gargadin cewa talla a kan tituna na ƙara jefa yara mata cikin haɗari.
Ta kuma ce yawaitar bayar da belin waɗanda ake tuhuma da fyaɗe na hana waɗanda abin ya shafa samun adalci, tare da jaddada cewa irin waɗannan laifuka kan yi wa lafiyar tunani da makomar yara mummunar. illa.
Kwamishiniyar ta ce an kwashe yarinyar zuwa wani wuri mai tsaro, kuma za a ba ta kulawar lafiya da ta ƙwararru, yayin da ma’aikatar ta ce za ta ci gaba da bibiyar shari’ar domin tabbatar da cewa an yi adalci.