Jami’ar Legas UNILAG, ta tabbatar da cewa dalibanta da suka maƙale a ƙasar Sin, bayan kammala shirin musayar karatu na tsawon shekara guda na kan hanyarsu ta dawowa Najeriya bayan jami’ar ta shiga tsakani.

Lamarin ya ɗauki hankalin jama’a ne bayan wani sako da aka wallafa a kafar X wanda ya bayyana cewa ɗaliban sun kasa komawa gida sakamakon matsalar tsarin tafiya, inda aka tsara musu tsayawar sa’o’i 27 a ƙasar Qatar, fiye da adadin lokacin da ake iya wucewa ba tare da bizar shiga ƙasar ba.

Rahotanni sun rawaito cewa matsalar ta samo asali ne daga yadda aka tsara tafiyar da lamarin da ya sa ɗaliban   suka maƙale a birnin Shanghai na ƙasar Sin.

Bayan haka an ce mataimakin shugaban jami’ar ya bayar da tallafin gaggawa domin kula da buƙatun ɗaliban tare da ɗaukar  matakan tabbatar da dawowarsu gida cikin koshin lafiya.

A cikin sanarwar da jami’ar ta wallafa a shafinta na X, ta ce an magance matsalar cikin gaggawa.

Sai dai mutumin da ya fara bayyana lamarin ya yaba da saurin martanin jami’ar amma ya buƙaci  a gudanar da bincike kan abin da ya haddasa matsalar.

Ya kuma yi zargin cewa malamin da ke jagorantar tafiyar ya yi wa daliban barazana saboda sun bayyana halin da suke ciki.

Ya zuwa yanzu jami’ar UNILAG ba ta fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen da ake yi wa malamin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *